Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin muƙamai.

Daga ciki ya naɗa Hon. Hisham Habib a matsayin shugaban gidan Rediyo Kano.


Gwamnan ya naɗa Alhaji Haruna Zago a matsayin shugaban hukumar kwashe shara daa tsafta ta REMASAB, sai Alhaji Abdullahi Rabi’u a matsayin shugaban hukumar raya birane.
Haka kuma gwamnan ya naɗa Injiniya Faisal Mahmud a matsayin shugabna hukumar Karota ta jihar Kano.
A wata sanarwa da mukaddashin babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Hisham Habib ya sanyawa hannu, gwamnan ya nada masu bashi shawara mutane shida.