‘Yan majalisa a Nigeriya sun zabi Opeyemi Bamidele a matsayin sabon shugaban masu rinjaye na majalisar Dattawa.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar na yau Talata.

Akpabio ya kuma bayyana sanata David Umahi matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Haka kuma Jam’iyyar APC ta amince da Mohammed Ali Ndume, matsayin mai tsawatarwa a bangaren masu rinjaye na majalisar dattijan.

Sai Sanata Oyelola Yisa Ashiru a matsayin mataimakin mai tsawatarwa a majalisar.

A zaman majalisar na yau Talata ne majalisar ta gudanar da wadannan zabubbubukan a bayan dawowar majalisar daga hutun bukukuwan bikin babbar sallah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: