Mazauna rukunin gidajen Trademore Estate a birnin tarayya Abuja sun gudanar da zanga-zanga akan tituna birnin bisa yunkurin rushe gidajensu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa mazauna rukunin gidajen da ke kan titin Lugbe zuwa filin jirgin sama sun fara zanga-zanga ne yayin da ma’aikatar Abuja ta fara shirin rushe gidajen yankin nasu.
Yunƙurin rushe gidajen na zuwa ne bayan wata mummunar ambaliyar ruwan sama da ta faru a rukunin gidajen sakamakon ruwan sama da aka yi mai yawa a safiyar ranar Jumu’a, 23 ga watan Yuni.

Ma’aikatar ta bayyana cewa sun yanke rushe rukunin gidajen bisa barazanar sake ambaliya a kai a kai a yankin.

Ma’aikatar ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su tattara kayansu ya sauya gurin zama.
Bayan sanarwar da ma’aikatar ta bai’wa mazauna yankin su ka gudanar da zanga-zangar a ranar Litinin akan nuna kin amincewa da matakin.
Saidai masu zanga-zangar sun bukaci da mahukuntan birnin cewa da a rushe musu gidajen gara ma’aikatar ta samo hanyar warware matsalar daga kwararrun injiniyoyi.
Idan ba a manta ba ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja FCTA ta ayyana gidajen Trademore da yanki mai cike da haɗari a birnin.