anata mai wakiltar Osun ta Gabas a Majalisar Dattawa kuma tsohon mataimakin kwanturola janar na hukumar kwastam Sanata Francis Fadahunsi yayi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya bude iyakokin Najeriya da aka rufe domin daidaita tattalin arziƙin kasar.

Sanata Fadahunsi ya bayyana hakan ne a gurin taron nuna godiya bisa sake zaɓarsa da aka yi.

Fadahunsi ya bayyana cewa rufe iyakokin Najeriya da tsohuwar gwamnatin Buhari ta yi ya kawo nakasu ga tattalin arziƙin.

Sanatan ya kara da cewa sake buɗe iyakokin zai kawo sauya fasalin tattalin arzikin Kasar, kuma ya tabbatar da cewa gwamnatin Bola Tinubu na da damar sauya tattalin arziƙin.

Ya ce abubuwa da dama sun taɓarɓare a Najeriya a halin yanzu tattalin arziƙin ƙasa ya yi ƙasa, Inda ya ce matukar gwamnati ta bude iyakokin za ta samu damar farfaɗo da tattalin arzikin Kasar da ya koma baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: