Kungiyar masu sayar da biredi a Najeriya PBAN ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin kara farashin kudin biredi sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin Kasar ta yi.

Shugaban kungiyar masu sana’ar biredi a Najeriya injiniya Emmuel Onuorah shine ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da jaridar Vanguad.

Emmanuel ya ce mafiya yawan kayan da ake hada biredin shigowa da su ake yi Najeriya wanda hakan yake da alaka da farashin naira a kasuwanni.

Shugaban ya kara da cewa rashin karin farashin biredin zai kawo nakasu ga cinikayya, inda kuma hakan zai haifarwa wasu gidajen biredin kullewa.

Emmnuel ya ce karin ya zama dole wanda hakan ne zai kawo musu mafita a cikin sana’ar ta su ta sayar da biredi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: