Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa ta jero wasu garuruwa a jihohin Najeriya da ake da yiwuwar fuskantar ambaliya.

 

A rahoton Daily Trust na ranar Laraba, an samu labari cewa amabliyar ruwan da za ayi fama da ita a shekarar nan. Za ta shafi jihohi 14.

 

Wannan annoba za ta shafi kusan 40% na jihohin kasar nan kamar yadda sanarwar da hukumar ta NEMA ta fitar a makon nan ya nuna.

 

Jawabin jan-kunnen ya fito ne daga ofishin Mista Ibrahim Farinloye wanda yake kula da harkokin NEMA a ofishinta na shiyyar Legas.

 

Ibrahim Farinloye ya bukaci wadanda abin ya shafa a jihohin da aka ambata su dauki matakai na rigakafi domin kare rayuka da dukiya.

 

Idan an samu irin wannan masifa, ya kan zo da asarar dukiya na gidaje, amfanin gona har zuwa rayukan dabbobi da kuma Bil Adama.

 

Jaridar ta ce an kawo garuruwan da ake tunanin za a iya ambaliyar, kuma bincike ya nuna annobar za ta fi aukuwa ne a yankin Arewa.

 

Delta da Akwa Ibom ne kurum jihohin yankin Kudancin Najeriya da za a fuskanci amabaliyar ruwa nan da wasu ‘yan kwanaki kadan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: