Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Nigeriya ta zargi jam’iyya mai mulkin kasar ta APC da laifin neman tursasawa majalisar akan zaben shugaban marasa rinjaye.

Jam’iyyar ta PDP ta bayyana haka ne gabanin dawowar majalisar hutun bukukuwan sallah babba ta bana.

Majalisar dattawan dai za ta dawo daga hutun ne a yau Talata inda ake sar ran majalisar za ta ci gaba da zaben shugabannin ta a zaman ta na yau.

Sai dai jam’iyyar ta PDP ba ta tantance wadanda za su tsaya mata takarar matsayin shugabanin masu rinjaye dana marasa rinjaye ba.

Abdul Ningi sanata daga jam’iyyar ta PDP ya ce
sun yanke shawarar cewa zasu aikewa da shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio wasika akan cewa kawo yanzu jam’iyyar ba ta cimma matsaya akan wadanda za su shugabanci majalisar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: