Gwamnatin jihar Taraba ta sanar da rage kudin makaranta ga daliban jami’a da kaso 50 cikin 100 domin ragewa daliban jihar radadin janye tallafin man fetur.

Kakakin gwamnan jihar Emmanue Bello shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, in da ya ce ya bada sanarwar ne a jami’ar jihar tare da jadda mahimmanci ilmi a gwamnatinsa.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tuni ya sanya dokar ta baci a bangaren ilmi a jihar.

Sanarwar ta cigaba da nuna damuwar gwamnan jihar Agbu Kefas wajen samar da ilmi firamari da na sikandire kyauta a jihar.

Dalibai da dama ne suka nuna jindadin su da wannan kuduri na gwamnatin jihar a inda suka bayyana cewa wannan ragi zai taimakawa harkokin karatunsu tare da sanya walwala a tsakanin daliban.

Kakakin na gwaman ya kuma bayyana cewa tsare-tsare sun kammala domin biyan ‘yan fansho da tsofaffiin ma’aikata hakkinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: