Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta, bayar da belin Abba Kyari a kan kuɗi naira miliyan 50.

Sai sai an bayyana cewa ba za a saki dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ba duk da wannan beli nasa da aka bayar.
Abba Kyari, wanda ke fuskantar tuhuma kan ƙin bayyana kadarorinsa tare da ‘yan uwansa, ya samu beli a ranar Alhamis.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta gurfanar da DCP Kyari da ‘yan uwansa Mohammed Baba da Ali a gaban kotu.

Hukumar ta cike tuhume-tuhume 24 kan Abba sakamakon ƙin bayyana wasu kadarori da ake zargin suna da alaka da shi.
A kwanakin baya ne aka ba da belin ‘yan’uwan Kyari da ake zargi da karɓar kuɗaɗe daga ƙasurgumin ɗan damfara, Ramoni Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, wanda aka alaƙanta da Abban.
A hkuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a James Omotosho ya bayar da belin Kyari a kan kuɗi miliyan 50 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Mai shari’a Omotosho ya ƙara da cewa, dole ne waɗanda za su tsaya masa su mallaki kadarar da ta kai ta naira miliyan 25 a inda kotun ke da iko.