A yayin da Shugaba Tinubu ya daura damarar yaki da ta’addanci domin cika alkawarin da ya daukar wa ‘yan Najeriya na kawo karshen matsalar tsaro, tsohon Gwamnan farar hula na farko a Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana cewar sasantawa ne kawai mafitar shawo kan ta’addancin.

Yarima wanda ya kaddamar da shari’ar Musulunci a Zamfara a shekarar 2000, ya bayyana wa Shugaba Tinubu cewar sasantawa da ‘yan ta’addan shi ne zai kawo karshen ayyukan ta’addanci a Zamfara da sauran Jihohin Arewa- Maso- Yamma da lamarin ya yi kamari.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da Shugaban Kasa a Abuja a farkon makon nan.

A cewarsa zaman sulhu da ‘yan bindigar shi ne zai kawo zaman lafiya a yankin Arewa.

Yariman Bakura ya bayyana cewar sulhun da yake bukatar a yi kwatankwaci ne da irin shirin afuwar da Shugaba Umaru ‘Yar’Adua ya yi da ‘yan ta’addan yankin Neja- Delta wanda a cewarsa ya haifar da da mai ido.

Manema labarai sun ruwaito cewar a shekarar 2009, Shugaba ‘Yar’Adua ya aminta da sulhu da ‘yan ta’addan yankin Neja- Delta da ke da albarkatun mai domin kawo karshen satar danyen mai da garkuwa da ma’aikatan mai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: