A yau Asabar shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai tashi izuwa kasar Guinea Bissau.

Shugaban za je kasar Bissau don halartar taron hukumar raya tattalin arziki karo na 63 na kasashen yammacin Afrika ECOWAS.

Kamar yadda kakakin shugaban Dele Alake ya bayyana a cikin wata sanarwa inda ya ce taron zai gudane a ranar Lahadi.

Ya ce za a tattauna muhimmam batutuwa da suka shafi sha’anin tsaro da kudi da kuma kasuwannci.

Sauran abubuwan da ake saran za a tattauna sun hada da rahoto akan sauyin gwamnati a jumhuriyyar Mali Burkinafaso da kuma Guinea.

Shugaban zai ta fi ne da wasu daga cikin masu ba shi shawara a gwamnatinsa .
Ana saran Shugaban Najeriya zai dawo gida da zarar an ankammala taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: