Hukumar dakille cututtuka masu yaduwa NCDC ta bayyyana cewa an samu sabuwar annoba da ta balle a Najeriya.

kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta ta ce wata cuta mai suna makarau ta hallaka mutane 80 a kasar.

NCDC ta ce cutur ta makarau ta halllaka mutane 80 kuma ta kama mutane 798 a fadin kasar.

Cikin inda cutar ta fi tasiri kano da katsina da kuma wasu jihohi a kasar.

Sannan cutar kamar yadda aka bayyana ta fi kama yara kanana da kuma manyan mutane.

An bayyana cewa cutar ta kewaye kananan hukumomi 33 a jihohi takwas harda babban birnin tarayya.

Alamominta sun hada da sarkewar numfashi zazzabii da kuma kumburin wuya da canzawar launin fata da yoyon majina.
NCDC ta ce za a iya kare kai ne idan mutum yana zuwa don karbar rigakafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: