Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ta ceto akalla mutane 63 daga hannun yan bindiga.

Shugaban Rundunar Sojin hadrin Daji masu yaki da yan ta’adda a yankin Arewa Birgediya Ahmad ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Ahmada ya ce akalla rundunar su ta soji mai yaki da ta’addanci a yankin arewa ta ceto mutanen da yan bindiga su ka yi garkuwa da su a cikin kwanaki Tara.

Ya ce nasarar ta samu ne a kwanaki Tara cikin jihohin Kebbi da Zamfara.

Birgediya Ahmad ya ci gaba da cewa yanzu haka sun mike tsaye don fatattakar yan bindiga daga yankunan.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka alumma suna cikin yanayin damina don haka dole rundunar ta tashi tsaye wajen yaki dan yan bindigar don barin mutane su yi noma a gonakinsu.

A cewarsa daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne yadda wasu zauna gari banza ke bayar da bayanan soja yan bindiga na tserewa.

Amma ya ce sun san akwai wadanda ake tursasawa suna bayar da bayanai.

Daga karshe ya rufe da cewa za su ci gaba da yakar yan bindigar yankin arewa da suka addabi jama a.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: