Aƙalla mutane 30 aka ceto daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kebbi.

An ceto mutanen a yankin Danko Wasagu a jihar bayan an yi garkuwa da su.

Mutanen da aka ceto sun fito ne daga yankunan Kontogora, dan Danmari da kuma Kaba sai wasu da su ka fito a Kajiji da Bena a jihon Zamfara da Kebbi.

Shugaban ƙaramar hukumar Danko Wasagu Alhaji Usman Bena ya tabbatarwa da manema labarai faruwar hakan.

Sannan ya yabawa gwamnatin jihar dangane da ƙoƙarin da ta yi don ganin ta ci gab ada kuɓutar da mutane tare da hana ayyukan ta’addanci a jihar.

Gwamnatin jihar ta sha alwashin kawo karshen masu satar mutane a jihar da ma makobtansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: