Gwaamnan jihar Ondo Rotimi Akeredelu ya ƙara wata guda domin zama a ƙasar waje sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sanarwa ƙarin wa’adin da aka aikewa majalisar dokokin jihar.

Gwamnan ya tafi ƙasar waje a ranar 5 ga watan Yuni kuma ake sa ran zai dawo a watan Yuli.

Ya mika ragamar mulkin jihar a hannun mataimakinsa bayan matsin lamba da ya samu daga jamiyyar adawa a jihar.

A yau Litinin shugaban majalisar dokokin jihar Hon Olamide Oladiji ya tabbatar da ƙara wa’adin wata guda da gwamnan ya sanar da su.

Ya ce matakin da gwamnan ya dauka na sanar da su ya na cikin doka.

Sannan ya yi fatan gwamnan ya dawo gida Najeriya ba da dadewa ba.

A shekarar 2024 ake sa ran za a sake zaben gwamna a jihar Ondo da ke Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: