Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa akalla kananan yara 300 ne suka mutu wasu suka bace a cikin shekara da muke ciki a kokarinsu na tsallaka tekun Baha Rum zuwa Turai daga arewacin Afirka.

A wani rahoto da hukumar kula da kananan yara a Majalisar Dinkin Duniya Unicef ta fitar ta bayyana cewa jirage da yawa sun kife a cikin ruwan wasu kuma da dama sun bace ba tare da an gansu ba.

UNICEF ta bayyana cewa bacewar wasu mutanen ya sanya ba za a iya gano adadin yaran da lamarin ya rutsa dasu ba.

Hukumar ta ce ya zama wajibi da a tashi a kara sanya dokokin da za su bai ‘wa kananan yara kariya tare da kubutar da rayuwar su daga fadawa hatsari.

UNICEF ta kuma yi kira da a kara samar da hanyoyin magance matsalolin da ke haddasa wa dumbum kananna yara barin muhallansu tare da sanya rayuwarsu cikin hatsari a yayin da su ka shiga cikin tekun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: