Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta kama wasu mutane 13 ’yan kasar China da ake zargi da hakar ma’adanai ta haramtacciyar hanya a Jihar Kwara.

Kwamandan hukumar ta EFCC shiyyar Ilorin Michael Nzekwe ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
Michael ya ce an kama mutanen ne a ranar Laraba a cikin Gandun Dajin Gwamnatin Jihar dake garin Ilorin a Jihar.

Kwamandan ya kara da cewa daga cikin mutanen 12 maza ne yayin da ya kasance mace daya.

Nwekwe ya bayyana cewa an samu nasarar kama su ne bayan samun bayanan sirri da aka samu akansu ba tare da sun biyan haraji ga Gwamnatin Tarayya ba kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Kwamandan ya ce a binciken da suka gudanar akansu sun gano cewa kafin a kama matanen sun riga da sun gama mamaye mafiya yawan dukkan Kananan Hukumomi 16 na Jihar, ta hanyar hakar ma’adanai ba tare da neman umarni ba.
Kazalika ya ce ya zuwa yanzu sun fara gudanar da bincike domin gano maboyar wasu ’yan Najeriya da ke hakar ma’adanan ba bisa ka’ida ba tare kuma da gurfanar da su gaban kotu domin yi musu hukunci.