Majalisar wakilan Najeriya ta amince da yiwa kundin kasafin kudin shekarar 2022 da ta gabata kwaskwarima.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa bayan gabatar da kudirin ba tare da bata lokaci ba majalisar tarayya ta amince da kudirin da ya fito daga fadar shugaban kasa ba tare da wata doguwar muhawara akansa ba.
A yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar Alhamis shugaban masu rinjaye a majalisa Hon Julius Ihonvbere ya ce bayan gabatarwa da majalisar rahoton sauran mambobin majalisar su ka amince da batun.

Yan majalisar wakilan sun amince da wata takarda da shugaban kasa ya aike masu a ranar Alhamis,inda ya nemi da a bai’wa gwamnatinsa damar kashe wasu kudade har Naira biliyan 819 da ba sa cikin kasafin kudi.

A cikin kudin da shugaban ya nemi amincewar majalisar ‘yan majalisa za su amfana da Naira biliyan 70 daga ciki,yayin da talakawan Kasar suma za su samu nasa kasafin da sauran ma’aikatun gwamnatin.
Mataimakin shugaban Majalisar ya bayyana cewa kudin da gwamnati za ta ware musu zai tafi ne wajen walwalarsu da sauran matsalolin da suke samu a bakin aiki.