Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Nairobi, kasar Kenya, a yau Asabar, 15 ga watan Yuli domin halartar taron tsakiyar shekara na gamayyar kungiyoyin hadin kan Afrika.

Kakakin shugaban kasar, Dele Alake, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuli.

Ya ce a matsayinsa na shugaban ECOWAS,Tinubu zai bi sahun sauran shugabannin kasashe da ministocin harkokin wajen kasashen Afirka da sauran manyan masu fada aji zuwa wajen taron da za a yi a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli.

Ya kuma ce shugaban kasa Tinubu zai gabatar da wani rahoto kan irin ci gaban da kungiyar ta samu cikin watanni shida da suka gabata a bangaren kasuwanci,walwala, zuba jari, samar da ababen more rayuwa, zaman lafiya da tsaro tsakanin kasashen yankin.

Taron zai hada shugabanni daga Comoros, Botswana, Burundi, da Senegal da kuma shugabannin sauran rassan kungiyoyin tattalin arziki takwas.

A cewarsa, wadannan kungiyoyi na tattalin arziki sun hada ECOWAS karkashin jagorancin Najeriya, kungiyar kasashen gabashin Afirka (ECA), kungiyar ci gaban gwamnatocin kasa da kasa (IGAD), Kungiyar kasuwancin bai daya ta kasashen gabashi da Kudancin Afirka (COMESA).

Sauran sune kungiyar kasashen kudancin Afirka ta (SADC), kungiyar kasashen yankin Sahel (CEN SAD, Kungiyar kasashen yankin Magreb (UMA), da kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka ta tsakiya (ECCAS).

Leave a Reply

%d bloggers like this: