Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa sanata Abubakar kyari ya zama mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da shugaban jam’iyyar APC na kasa sanata Abdullahi Adamu yayi.

A kundin tsarin mulkin jam’iyyar mataimakin shugaban jam’iyyar ne zai maye gurbin shugaban jam’iyyar Idan ya sauka daga kan mukamin sa a matsayin mukaddashin shugaba.

A halin yanzu Sanata Abubakar kyari yana jagorantar taro da wakilan kwamitin jam’iyyar APC na kasa a shelkwatar jam’iyyar dake birnin tarayya Abuja cikin tsauraran matakan tsaro.
Daga cikin wanda suka halarci taron sun hadar da mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar kudancin kasar Emma Unukwu dana shiyyar arewa maso yamma salihu lukman dana arewa maso gabas Salihu Mustapha dana arewa ta tsakiya Muazu bawa dana kudu maso yamma issacs kekemeke dana kudu maso gabas ejoroma aradiogu da mataimakin sakataren jam’iyyar na kasa Barr festus fuanter.