Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya rantsar da wasu kwamishinoni uku a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jihar.

Da yake jawabi jim kadan bayan rantsar da su Engr. Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabbin kwamishinonin da su kasance masu jajircewa, sadaukarwa da gaskiya ya yin gudanar da ayyukansu.

Ya ci gaba da cewa nadin nasu ya kasance bisa cancanta da kuma gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.

Gwamnan ya bayyana sunayen su da mukaman sabbin kwamishinonin kamar haka.

1. Alh. Ibrahim Jibril (Provost) – bangaren Kudi.
2. Alh.Ibrahim Namadi Dala – Kulawa da Tattalin Arziki
3. Haj. Amina Abdullahi Sani (H.O.D) – Ayyuka na Musamman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: