Hukumar yaki da sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta kama wata lauya da ta kware wajen hadawa da kuma safarar miyagun kwayoyi a Jihar Legas.

 

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

 

Femi ya bayyana cewa wadda ake zargin mai suna Ebikpolade Helen mazauniyar yankin Lekki ce da ke Jihar ta Legas, ta kware ne wajen hade-haden miyagun kwayoyi daban-daban da suke sanya mutane maye.

 

Kakakin ya kara da cewa sun samu nasarar kama lauyar bayan samun bayanan sirri da suka yi akanta a Awka babban birnin Jihar Anambra.

 

Inda suka kwace kilogiram biyar na ganyen tabar wiwi da kuma kwalaban kayan maye 12.

 

Kazalika Femi ya kara da cewa hukumar ta sake kama wani matashi mai suna Abubakar Shu’aibu a ranar 13 ga watan Yuli a kan hanyar Mushin-Oshodi da ke Jihar Legas dauke da kwalaben Kodin 86.

 

Babafemi ya ce nauyin kayan mayen da aka kama a gurin matashin a cikin motarsa ya kai lita 8.6.

 

Sannan ya ce hukumar ta kuma kama wasu mutane biyu a ranar 11 ga watan Yuli a Ikorodu.

 

Inda ya ce dukkan su bayan kammala bincike akansu hukumar za ta aike da su gaban kotu domin yi masa hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: