Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da shugabannin ƙasashen Afirika uku masu makwabtaka da Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

Takwarorin shugaban ƙasar da suka kawo masa ziyara sun haɗa da Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin, Umaro Sissoco Embalo na Guinea-Bissau, Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar.
Har ya zuwa dai lokacin kammala haɗa wannan rahoton ba a bayyana haƙiƙanin dalilin ganawar shugabannin ba.

Shugabannin ƙasar waɗanda suka iso fadar shugaban ƙasar da rana, ana sa ran za su tattauna muhimman batutuwan tattalin arziƙi da Shugaba Tinubu.

Shugabannin sun iso ne a lokuta mabanbanta inda Shugaba Tinubu ya yi musu maraba a harabar ofishin sa.