Kungiyar malaman kwalejin ilimi a Najeriya sun bai wa mambobinsu umarnin fara zuwa aiki sau biyu a mako.

Hakaan na zuwa ne bayan da aka sake kara farashin litar man fetur a kasar wanda hakan ya kara tsadar zufuri.
Shugaban kungiyar na kasa Dakta Sam Olugbeko ne ya sanar da umarnin tare da sanar da cewar za su fara zuwa makarantu sau biyu a mako har sai gwamnatin tarayya ta yi bayani a dangane da hakin da ake ciki.

Sannan kungiyar ta ce ba za su koma aiki a ranakun aiki baki daya ba sai gwamnatin ta rubanya albashinsu da kashi 200 domin rage radadin halin da ake ciki na tsadar fetur.

Kungiyar ta ce farashin kitar mai ya rubanya da kaso 250 cikin watanni biyu na sabuwar gwamnatin, wanda hakan ya haifar da tsadar kayan abinci, sufuri, da sauran al’amuran yau da kullum.
A ranar Takata ne aka sake samun karin farashin kitar mai a Najeriya wanda ake siyar da shi a kan naira 617 zuwa 630 kowacce lita.