Ƙungiyar dilallan man fetur a Najeriya ta ce har yanzu ana shan mai da arha a Najeriya la’akari da sauran kasashen Afrika.

Mai magana da yawun kungiyar Yakubu Suleiman ne ya bayyana haka ya ce ko da wannan karin farashin da aka samu a kwanan nan a Najeriya farashin litar man na da arha.


A wata ganawa da yayi da Arise TV dangane da hawan farashin litar man, ya ce duk da ƙarin farashin da aka samu ana shan man fetur cikin sauƙi a Najeriya.
Sai dai Suleiman ya alakanta tashin farashin litar man da aka samu ranar Talata da hauwan farashin dala.
Ya ce wajibi ne a dinga fuskantar hawa ko saukar farashin man la’akari da yadda ake siyar da danyen mai a kasuwar duniya.
Sai dai ya ce sam dilallan man ba sa farin ciki da tashin farashin da ake samu.
Sannan ya ce kaf kasashen Afrika Najeriya na da mafi sauƙin man.
Sai dai ya ce ba sa fata farashin ya sake darawa dag ayadda yake a yanzu.
A ranar Talata ne dai aka wayi gari da sabon farashin litar mai wanda ta koma naira 617 zuwa 630 maimakon naira 540 da ake siyarwa.
Farashin man ya kai naira 540 kan kowacce lita bayna da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a Najeriya a jawabin da yayi jim kaɗan bayna rantsar da shi.