Shugaban kungiyar tsimi da tanadi na ma’aikatan asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), Malam Kabir Abba Yakasai ya bayyana cewa, kungiyar na yunkurin kafa bankin kanta, domin bayar da kananan basuka ga kananan masana’antu da marasa karfi.

 

A cewarsa, an kafa kungiyar tsimi da tanadi ne a 2002, domin hada kai da taimakon juna na ma’aikatan asibitin koyarwa na Aminu Kano, kuma zuwa yanzu tana da mambobi 1909.

 

Ya ce a shekaru 22 da kungiyar ta yi, mambobinta sunci gajiyar wannan gamayya ta tsimi da tanadi na ma’aikatan ta hanyar mallakar gida, fili ko mota da sauransu.

 

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a da ta gabata a Jihar Kano.

 

Ya ce idan aka yi la’akari da daruruwan babura da motoci da gidaje da filaye da kayan abinci da wadannan ‘yan kungiya ke amfana da ita, to lalle akwai bukatar duk inda ma’aikata suke na gwamnati ne ko na kamfanoni su yi kokari su kafa irin wannan kungiya domin amfaninta ga ma’aikata.

 

Ya ce ita dai wannan kungiya ta hadin kai tana samun kudinta ne ta hanyoyi kamar uku da suka hada da daukar kashi goma cikin 100 na riba na abin da kungiyar tasaya wa ma’aikaci ga mai bukata, sai biyan naira 200 ga duk dan kungiyar da kuma ribar hannin jari da aka sa a kungiyar ko aka siyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: