Rundunar ‘yan sandan Jihar Nasarawa ta samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar mota a cikin karamar hukumar Lafiya da ke Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar DSP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Lafiya babban birnin Jihar.


Nansel ya kara da cewa bayan wadanda ake zargin masu shekaru 49 da 38 sun sace motar sun tsere ne zuwa Jihohin Taraba da Filato.
Kakakin ya ce sun samu nasarar ne bayan jami’an sun dukufa wajen tsananta bincike akan mutane.
Kakakin ya kara da cewa sun kama mutanen ne a ranar 19 ga Yulin da muke ciki da misalin karfe 4 na yammaci bayan shigar musu da rahotan satar motar.
Nansel ya ce wadanda su ka shigar da karar sun bayyana cewa sun bai wani mai gyara motar ne,daga bisani wadanda ake zargin suka yi awon gaba da ita.
Jami’in ya ce bayan shigar musu da rahotan ne su ka aike da jami’ansu da ke aiki a wani sashen na jami’an ‘yan sandan Lafiya inda suka fara gudanar da bincike.
Kakakin ya bayyana cewa bayan binciken da jami’an su ka gudanar ne suka yi nasarar kama Sani Labaran mai shekaru 49 a garin Gembu da ke Jihar Taraba,inda ya shaida musu cewa shi dan asalin Titin Shinge ne da ke garin Lafiya Jihar Nasarawa.
Sannan ya kara da cewa Jami’an sun kama abokin aikin nasa Ibeto Nwobedo mai shekaru 38 wanda ya kasance dan garin Faringada ne da ke jihar Filato a garin Jos babban birnin Jihar.
Nansel ya ce da Zarar sun kama bincike akan su za a gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci.