Wata kungiya a Jihar Edo sun gudanar da zanga-zanga akan titunan babban birnin Jihar domin nuna kin amincewa da karin farashin man fetur da aka yi a Kasar.

 

 

Channels TV ta rawaito cewa masu zanga-zangar sun bi ta wasu manyan tituna Jihar ,inda su ke Allah-wadai da karin farashin Man da kuma tsadar rayuwa a fadin Kasar.

 

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa karin farashin abin takaici ne, tare da sukar matakin karin farashin man fetur din yayin da ake ci gaba da fuskantar tsananin talauci a Kasar.

 

Masu zanga-zangar da ke dauke da kwalaye masu rubutu daban-daban, sun kuma yi watsi da shirin tallafin Naira 8,000 da Gwamnatin Tarayya ke yi shirin bai’wa ‘yan Kasar bayan cire tallafin man fetur.

 

A halin yanzu a Najeriya ana ci gaba da fuskantar tsananin da tsadar rayuwa bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta cire tallafin Man fetur wanda hakan ya haifar mata da suka ga ‘yan Kasar akan yadda ta ke tafiyar da mulkin Kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: