Masu shirya fina finai a Arewacin Najeriya sun koka bisa halin rashin hanyoyin samun kudi a masana’antar Kannywood, inda a yanzu akafi maida hankali akan YouTube a matsayin hanyar samun kudi ta farko, sun bayyana hakan a matsayin koma baya.

Masana Harkokin shirya Fina Finai a Arewacin Nigeriya ne suka Shirya Wani taro na yini biyu, domin farfado da Martabar Shirya Fina Finai a Arewacin Nigeriya.


Taron da aka yiwa take da da Northern Film Summit, wanda aka gudanar a jahar Kano, ya samu halartar masana, shugabannin bangarori daban da ban na Kannywood, wanda suka hadar da Masu Shiryawa da Jarumai, da Masu harkokin Rubutun Labarai a Masana’antar.
Lokacin da yake Jawabin a wajen taron, wanda shine ya jagoranci shirya taron a Kano Isreal Kashim Audu mamallakin Kaduna International Film festival, (KADIFF) ya sheda cewa sun shirya Taron ne domin wayar da kan Masu sana’ar Fina Finai, akan yadda za’a bun kasa harkokin fina finai a samar da cigaba ta yadda Kannywood zata fara gogayya da duk masana’antun shirya fina finai na Duniya.
Isreal ya ce akwai cigaba sosai a Arewa Musamman yadda Ake samar da labari da kuma shirya Fina Finai, haka Kuma akwai Kalubale masu tarin yawa wanda ya kamata ace an gyara.”
Audu ya Kara da cewa basa Jin dadin yadda ‘yan wasan kwaikwayo suke mayar da kan su baya, acewarsa duk wani abu da ake shiryawa na taro domin tattauna matsalar Fina Finan Hausa, Jarimai da masu shiryawa harma da masu bada umarni da yawansu basa halarta duk kuwa da cewa an shirya ne saboda su.
“Duk da rashin zuwan wadanda muka shirya taron domin su, gwiwoyina ba za suyi sanyi ba domin nasan zan iya fuskantar wannan kalubalan, dama ban fito ba sai da na shirya fuskantar ko wane irin kalu bale”.
Acewarsa sun zabi shirya taron ne a Kano domin itace cibiyar shirya fina finan Hausa.
A Jawabin Shugaban NOWA Kuma Marubuci Ado Gidan Dabino yace Taron na Northern Film Summit yazo akan gaba, Sai dai Kuma akwai rashin bawa Hausawa damar yin aikin da ya kamata a harkokin film, domin gurare da yawa ana tauye yan film din Hausa wannan Yana taimakawa su dinga ja baya daga wasu harkokin.
Ado Gidan Dabino ya Kara da cewa, akwai Matsaloli da suke fuskanta Wanda dole Sai Gwamnati ta hada Kai dasu za,a kawo gyara, tunda dai sune keda da basira.
Kamal S Alkali Mai shirya Fina Finai, Mai bada Umarni kuma marubuci, ya shaidawa Mujallar Matashiya cewa akwai bukatar Gwamnati ta kula da Masana’antar Kanywood domin kawo cigaba a cikin sana’ar.
Yayi Kira ga Jariman Masana’antar Kanywood dasu dukufa wajen neman ilimi, tare da yawan karance karance, domin hakan zai basu Nasara a aiyukan da suka sanya a gaba.
Mujallar Matashiya ta rawaito cewa taron na Northern Film Summit ya samu Halartar Manyan Baki daga kashi daban daban, domin tattauna matsalar Fina Finai a Nigeriya musamman Arewacin kasar.