Kungiyar Progressive Union of Southern Nigeria (PUSSON), kungiyoyi masu zaman kansu sama da 50 daga dukkan shiyyoyin siyasa uku na Kudancin Najeriya, sun taya tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje (CON), murnar samun nasarar goyon bayan shugaba Bola Tinubu tare da sauran masu ruwa da tsaki domin ya zama shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa.

A wata wasika da aka hada hannu da Kodinetan kungiyar, Mista Frank Idowu Dele da Sakatariyar, Misis Grace Okechukwu kuma suka mika wa Ganduje, ‘yan mintoci da suka gabata, sun bayyana jin dadinsu da fitowar sa tun da farko.


A cewar wasikar, zaben Ganduje na zama shugaban jam’iyyar shaida ne karara kan yadda tsohon gwamnan ke da amana da biyayya ga shugaba Tinubu da tsarin siyasar jam’iyyar.
Da yake jaddada cewa, fitowar Ganduje zai taimaka wa dimokuradiyyar cikin gida da kuma zurfafa sanin siyasa a cikin jam’iyyar, domin ci gaban siyasar kasa baki daya.
Ya kara da cewa, “A cikin wannan lokaci da jam’iyya mai mulki ke fama da rikici, lokacin da shugaban jam’iyyar na kasa da Sakatariyar jam’iyyar suka yi murabus, abin da jam’iyyar ke bukata shi ne wanda yake da gogewa a fagen siyasar jam’iyya, dimokuradiyya da kuma kyakkyawan alaka ga kowa.
Wasikar ta ce, lokacin da al’amura suka yi tsauri, ana bukatar gaskiya da amana, mai girma gwamna an bayyana cewa ya zama daya daga cikin amintattun jam’iyyar da za su dace da wannan mukami.
Da suke jinjina wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, saboda zurfin tunani da fahimtar da Ganduje yake da shi a fagen siyasar jam’iyya, sun ce, sauyin mai girma Gwamna ya nuna yadda Nijeriya da jam’iyya mai mulki musamman ke shirin saka masa da kishin kasa, sadaukarwa, jajircewarsa da rashin son kai.
Sun tuno da yadda yankin Kudancin kasar nan suka amince da shi, tun kafin yanzu, kishin Ganduje da jajircewarsa wajen gina kasa da hadin kan kasa ya ce suna iya tunawa da yadda suka ceto Najeriya daga fadawa cikin rudani a lokacin da suka sasanta tsakanin kungiyoyin Arewa da Igbo.
Sun ba da tabbacin cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta samu dimbin nasarori daga dimbin gogewar da ya yi, da salon siyasarsa, da biyayyar sa ga jam’iyyar da kuma zurfin fahimtarsa da fahimtar juna a cikin kasa.