Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya bayyana aniyar matakinsa na tura wa ƙasashen Afrika shida hatsi kyauta.

Putin ya bayyana hakan ne a wajen taron Rasha da ƙasashen Afrika da ke gudana a birnin St Petersburg.

A wajen taron, shugaba Putin ya ce nan da wasu ƴan watanni masu zuwa ne za su fara tura hatsin kyauta.

Hakan na faruwa ne bayan Rasha ta fice daga yarjejeniyar shiga tsakanin ta Ukraine ta Majalisar Dinkin Duniya.

Putin Ya ce a shirye Rasha take da cike duk wani giɓin hatsi da Ukraine ta haifar.

Ya kuma ƙara da cewa, a shirye Rasha take wajen samar da hatsi ga ƙasashen Afrika shida a cikin watanni uku zuwa huɗu masu zuwa.

Sannan watanni uku zuwa huɗu masu zuwa, Rasha za ta tura wa kowace ƙasa tan dubu 25 zuwa dubu 50 na hatsi.

Ƙasashen su ne, Burkina Faso, da Zimbabwe, da Mali, da Somalia, da kuma Afrika ta tsakiya, sai ƙasar Eritrea.

Putin ya ce Rasha zata tabbatar an tura hatsin kyauta ba tare da biyan koda kuɗin dako ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: