Ma’aikatan kamfanin ibom Air sun kama wani fasinjan mai suna Ogeneochuko David da ya sace Kwamfutar wani fasinja a cikin Jirgin da ya taso daga Legas zuwa Abuja a ranar 26 ga Yuli, 2023.

 

Ma’aikatan sun kama fasinjin ne bayan ya sace kwamfutar daya fasinjan a cikin Jakarsa a gurin da ake ajiye kaya a jirgin.

 

Mai kwamfutar ya bayyana cewa ya gano David ya sace masa kwamfutar ne a lokacin da ya ga yana kai kawo a cikin jirgin, wanda hakan ya sanya duba jakarsa.

 

Inda daga nan ne ya gano cewa an ɗauke masa kwamfutar wanda hakan ya sanya ya sanarwa da ma’aikatan cikin jirgin halin da ake ciki.

 

Ya ce bayan sanar da jami’an aka fara gudanar da bincike wanda har ta kai ga an gano kwamfutar a wajen Mista David.

 

Bayan kama wanda ake zargin kakakin kamfanin ta ce nan take aka sauke David tare da miƙa shi ga jami’an tsaro na Hukumar Kula da Jiragen Sama na Tarayya FAAN domin gudanar da bincike akansa.

 

Kakakin ta kara da cewa daga bisani kuma aka miƙa wanda ake zargin zuwa ga jami’an ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.

 

Aniekan ta ce bayan jami’an ‘yan sanda sun gudanar da bincike ta tabbatar musu da cewa wanda aka kama dan wata babbar ƙungiya ce da ta ƙware wajen sata a cikin jiragen sama.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: