Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya sadaukar da kashi 50 na albashinsa ga wata gidauniya ta musamman domin talakawa, marasa karfi da gajiyayyu a Jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a gurin rantsar da kwamishinoninsa 14 bayan kammala tantancesu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi.


Uba Sani ya bayyana cewa tuni an yi nisa gurin shirin kaddamar da gidauniyar talakawa da marasa galihu a Jihar a yayin da ake kafa kwamitin da zai jagoranci tsarin tallafawa talakawan Jihar.
Gwamnan ya ce yayi hakan ne domin kawo karshen rage kashe kudaden gudanar da ayyukan gwamnatin Jihar domin tallafawa rayuwar talakawan.
Sanata Uba Sani ya kara da cewa yin hakan zai kawo karshen matsalolin da talakawan Jihar ke fama da su tare da tabbatar da walwalarsu.