Akalla fulani makiyaya 21 ne mayakan ISWAP su ka hallaka a wasu hare-hare daban-daban da suka kai Jihar Borno.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan sun kai harin ne akan wasu babura 17, inda su ka hallaka wasu makiyaya 14 a garin Kukawa a yammacin ranar Talata 25 ga watan Yuli, 2023 bayan sun zarge su da kai rahotonsu ga jami’an soji.


Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Kasar Chadi Zagazola Makama ya ce a yayin hallaka makiyayan ‘yan kungiyar ta ISWAP ba su yi amfani da bindiga ba gurin kashesu inda suka yi amfani da adduna gurin cire kawunan da dama daga cikin makiyayan.
Zogazola ya kara da cewa bayan hallaka makiyayan da kuma sace musu dabbobi, maharan su ka nufi hanyar kauyen Kukawa, Doro da kuma Kalla, yankunan da ’yan ta’adda da dama su ka mamayesu.
Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su suka tsere sun gano gawarwaki hudu daga ’yan uwansu da aka hallaka a cikin dajin.
Koda a makonnin da su ka gabata sai da shugabannin kungiyar ta ISWAP suka sanya dokar hana kamun kifi noma da kiwo a wasu yankuna na Jihar,bayan ‘yan ISWAP din sun zargin mutanen da yiwa jami’an soji leken asiri a kansu.