Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu mata akalla 23 a wani daji da ke Jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da matanen ne a wani daji da ke kusa da garin Damaga cikin Karamar Hukumar Maradun ta Jihar ta Zamfara.


Matan wadanda suka hada da ’yan mata sun shiga cikin dajin ne domin dibar itacen girki a lokacin ’yan bindigar da ke kan babura suka yi awon gaba da su zuwa cikin dajin.
Suma wasu rahotanni sun ce an yi garkuwa da mutanen ne kwanaki biyu bayan hallaka wasu sojoji bakwai da wasu manoma sama da 20 a Jihar a yayin wata musayar wuta tsakanin jami’an soji da wasu ’yan bindiga a kusa da kauyen Kangon Garucci da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar.
Wani mazaunin garin mai suna Ayuba Damaga ya ce sun gano matan nasu 23 na hannun ’yan bindigar amma har kawo yanzu ba su tuntubi ‘yan uwa da iyalan wadanda su ka yi garkuwa da su ba domin karbar kudin fansa ba.
