Mabiya mazhabar shi’a a Najeriya sun fita zanga-zanga a Kaduna kan rashin adalci da ake yi wa shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

‘Yan shi’an sun cika titin Ahmadu Bello a birnin Kaduna a jiya Juma’a 28 ga watan Yuli inda suke dauke da kwalaye da suke nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake muzantawa shugabansu.


A yayin zanga-zangar lumanar, matasan kungiyar sun yi shiga da bakaken kaya yayin da suke daga hannayensu sama.
Kakakin kungiyar, Injiniya Yunusa Lawal Musa yayin hira da ‘yan jaridu ya ce suna wannan zanga-zangar ne don nuna rashin jin dadinsu akan abubuwan da ake musu.
Ya ce sun yi hakan ne a manyan titunan birnin Kaduna don sanar da mahukunta irin rashin adalci da ake musu da kuma shugabansu.
Mabiya shi’a sun kuma bukaci a bar kowa ya yi addininsa kamar yadda dokar kasa ta tanadar akan ko wane dan kasa.
Ya ce idan har gudanar da addinin bai saba wata doka ta cikin kundin tsarin mulki ba, to dole kowa a ba shi ‘yancin yin addinin da ya ke so.