Hedkwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa an kama wani tsohon soja mai safarar makamai da sauran kayan aiki ga ƴan ta’addan Boko Haram a ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da daraktan watsa labarai na hukumar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar a ranar Juma’a 28 ga watan Yulin 2023.
Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an kama tsohon sojan ne a ranar 18 ga watan Yuli, a garin Boi cikin ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi.

Haka kuma daraktan watsa labaran ya bayyana cewa dakarun sojoji sun halaka ƴan ta’adda da dama a sassa daban-daban na ƙasar nan a cikin watan Yuli.

Buba ya bayyana cewa sama da ƴan ta’adda 700 waɗanda suka haɗa da ƙananan yara suka miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno.
Buba ya ƙara da cewa wani ƙasurgumin ɗan ta’addan Boko Haram mai suna Ali, ya miƙa wuya a hannun dakarun sojoji a Dogumba cikin ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.