Jam’iyyar PDP ta yi martani a kan zabar tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin minista.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum, ya ce jam’iyyar za ta dauki kwakkwaran mataki kan nadin Wike.
Damagum, wanda ya bayyana hakan a wata hirar waya da jaridar The Nation a ranar Juma’a. 28 ga watan Yuli, ya kara da cewar tuni suka fara tuntuba kan lamarin Wike.

Sannan ya musanta zargin cewa PDP ta yi bacci tun bayan sanar da sakamakon babban zaben 2023.

Ya ce babu wata tangarda a jam’iyyar PDP kamar yadda aka ce, don kawai ba a ga sun hau kan tituna ba, ana ci gaba da tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki ne a kan lamarin.