Hukumar kula da Shige da Fice ta Ƙasa shiyar Kano (Nigerian Immigration Service) ta sha alwashin haɗa hannu da Hukumar kula da zirga zirgar ababen Hawa ta Kano (KAROTA) wajen dakile shigowar baƙi Jihar Kano ta tashoshin Motoci ba bisa Ƙa’ida ba.

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa a jihar Kano Ahmad Dauda Bagari ne ya sha wannan alwashi yayin da ya karbi baƙuncin sabon Shugaban Hukumar (KAROTA) Engr. Faisal Mahmud Kabir a ofishinsa.
Bagari ya ce Hukumomin guda biyu tamkar Ɗan’juma ne da Ɗanjimmai wajan gudanar da ayyukansu.

Dauda Bagari ya ce ƙofar Hukumarsa (Nigerian Immigration service) a buɗe take wajen ganin an gudanar da aiki kafaɗa-da-kafaɗa da Hukumar (KAROTA) domin ciyar da jihar Kano gaba dama kasa baki ɗaya gaba.

Yana mai cewa Hukumarsa a shirye take wajen kula, tare da kama baƙin haure waɗanda suke zuwa ƙasar nan ta hanyar tashoshin mota ba bisa ƙa’ida ba.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ya ce Hukumar KAROTA a shirye take wajan gudanar da aiki tare da Hukumar kula da Shige da ficen.
Yana me cewa ya kai ziyarar ce domin sada zumunci da kulla alakar aiki duba da yadda ayyukan Hukumar ke da alaka dana Hukumar KAROTA, a don haka a shirye muke domin gudanar da aiki tare da nufin ciyar da harkar sufuri a fadin jihar nan gaba ɗaya.
A ƙarshe ya roƙi Hukumar da ta taimaka wajen bayar da horo ga jami’an KAROTA domin su gane baƙin haure waɗanda suka shigo jihar Kano ba bisa ka’ida ba.