Ƙungiyar kwadago ta fice daga wurin taron da aka shirya da wakilan shugaban ƙasa a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja ranar Jumu’a.

Daily Trust ta ruwaito cewa an shirya taron ne domin tattauna batun tallafin rage radaɗin da gwamnatin tarayya zata raba wa yan kasa bayan cire tallafin man fetur.


Joe Ajaero, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ya jagoranci tawagarsa zuwa ofishin shugaban ma’aikata, inda taron ya gudana, amma ba da jimawa ba suka fito daga Villa.
A ranar Laraba da ta gabata, kwamiti na musamman ya fara zama da wakilan gwamnatin tarayya kuma suka cimma matsayar dawowa ranar Juma’a domin jin ba’asi kan buƙatun NLC.
Gwamnatin tarayya ce ta kafa kwamitin domin duba hanyoyin da ya dace a bi na rage radaɗin cire tallafin man fetur ga ma’aikata.
Amma taron bai yuwu ba saboda ƙaranci halartar mutane inji wani mamban kwamitin.
Kungiyar kwadagon ta zargi gwamnatin tarayya da yin amfani da tarurrukan a matsayin hujja wajen yaudarar ‘yan Najeriya.
Wata majiya a wajen taron ta tabbatar da cewa, ya kamata wasu kananan kwamitoci guda uku da suka hada da kwamitin sufuri, kwamitin gas da kuma kwamitin raba tsabar kudi su halarci taron.
A cewarsa, ana buƙatar waɗannan kananan kwamitoci su hallara domin yi wa babban kwamitin bayanin matakan da aka dauka domin dakile illar tallafin man fetur ga ma’aikata.