Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rantsar da shugaban ma’aikatan jihar da wasu mutum biyu masu ba shi shawara na musamman.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa gwamnan ya kuma rantsar da shugabannin riƙon ƙwarya na ƙananan hukumomi 27 a jihar.


An gudanar da taron rantsar da sabbin masu muƙaman ne a ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, yayin da babban alƙalin alƙalai na jihar, mai shari’a Kashim Zannah, ya basu rantsuwar kama aiki.
Taron ya gudana ne ranar Juma’a, 28 ga watan Yuli a sakatariyar Musa Usman dake birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
Waɗanda aka naɗa muƙaman sun haɗa da Malam Fannami wanda yake lauya ne a matsayin shugaban ma’aikatan jihar, Haruna Hassan Tela, a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar.
Sauran sun haɗa da Isa Umar Gusau, a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai da tsare-tsare da Birgediya Janar Abdullahi Ishaq, a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tsaro.
Da yake jawabinsa a wajen taron, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa naɗin da aka yi musu, an yi musu shi ne bisa cancanta, gaskiyarsu da kuma ƙwarewar da suka nuna a fannoninsu.
Ya buƙace su da su gudanar da ayyukansu ba tare da wani tsoro ba ko yi wa wani ko wata alfarma.