Gwamnan jihar Adamawa Ahmad Fintiri ya sassauta dokar hana fita a jihar zuwa awanni 12.

Gwamna Fintiri ya sassauta dokar kamar yadda babban sakataren yada labaransa Humwashi Wonosikou ya sanar a babban birnin jihar.

Sanarwar ta ce an sassauta dokar ne daga karfe shida na safe zuqaa shida na yamma.

Sanya dokar da aka yi ya biyo bayan wasu matasa da ake zargi da ɓalle rumbun adana abinci na hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA reshen jihar Adamawa.
Gwamnatin jihar ta ce mutanen da su ka aikata hakna sun yi korafin yunwa da kuma tsadar kayan abinci.
Sai dai gwamnatin ta ce abin ya kazanta ganin yadda matasan su ka farwa yan kasuwa da makamai tare da sace kayyakinsu.
Gwamna Fintiri ya bukaci al’umma a jihar da su kasance masu bin doka da oda a jihar tare da jayar da gudunmawa don samar da zaman lafiya.