Majalisar dattawan Najeriya ta za ta tura wakilci don ganawa da shugaban ƙasa dangane da yunkurin yajin aikin da kungiyar kwadago ta kudiri aniyar yi ranar Laraba.

 

Hakan na zuwa ne bayan kudirin da wakili a zauren majalisar daga Kano Honarabul Abdurrahman Kawu Sumaila ya kai a zaman majalisar na yau.

 

Kawu Sulamila ya ankarar da majalisar a dangane da yunkurin yajin aikin da ake shirin farawa.

 

Kuma ya nuna damuwa a kan yadda hakan ka iya haifarwa da tattalin arziki koma baya.

 

Ya ce idan ba a magance matsalar ba, hakan na iya haifar da rasa rayuka a kasar.

 

Sai dai wani dan majalisa Jibril Isa daga jihar Kogi ya ce shugaban kasa ba ya murna da halin da kasar ke ciki.

 

Majalisar ta amince tare da tura wakilci don ganawa da fadar shugaban ƙasa a dangane da lamarin.

 

Kungiyar kwadago ta dauki aniyar tafiya yajin aikin ne a ranar Laraba dnagane da karin kudin man fetur da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: