Wani rahoto da ke fitowa na nuni da cewar ƙungiyar kwadago a Najeriya na iya janye yajin aikin da take shirin farawa a gobe Laraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda sakataren kungiyar na kasa Emma Ugbaja ke bayyana yuwuwar hakan bayan ganawa da wakilan fadar shugaban ƙasa a ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa yau a Abuja.
Emma ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta zauna tare da nazari a kan batun kafin ranar Laraba.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila ya bayyana kungiyar a matsayin wadda ke sauraron kowanne ɓangare kuma ba za ta gudanar da yajin aikin ba kasnacewar ta saurari shugaban ƙasa.

Kungiyar ta daura damarar tafiya yajin aikin ne a gobe Laraba da nufin sanar da masalaha ga jama’a.