Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya ce baya iya bacci sakamakon halin da yan kasar suke ciki na matsin rayuwa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatar ga yan kasar a yammaci Litinin a gidan talabijin kasa.

Shugaban ya ce halin tabarbarewar da bangaren koyo da koyarwa da harkar lafiya da rashin samun abubuwan more rayuwa ga talakawan kasar na daga cikin abinda suke hana shi rintsawa.

Da yake magana game da yajin aikin da kungiyoyin kwadago zasu shiga a ranar Laraba shugaban ya bukaci kungiyar da ta bashi lokacin domin ya bijiro da tsare-tsaren da zai ragewa yan kasar wahalhalun da suke sakamakon cire tallafin man fetur.

Kungiyar kwadago dai ta shirya tsunduma yajin aikin ne biyo bayan rashin gamsuwa da cire tallafin man fetur da shugaba Bola Ahmad Tinubu yayi a ranar 30 mayu 2023 bayan shan rantsuwar maka aiki a matsayin na sabon shugaban kasa.

%d bloggers like this: