Daga Jihar Legas kuwa wani jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad a jihar.

 

Ko da dai ba a gano jirgin ba amma an ceto mutane biyu da ake zargi matukan jirgin ne

 

Har yanzu ba a iya gano adadin mutanen da lamarin ya shafa ba sakamakon faduwar jirgin.

 

Ɓangaren gaggawa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta kasance a wajen domin bayar da agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

 

Har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari babu cikakken bayani daaga hukumomi a jihar bisa faruwar lamarin

Leave a Reply

%d bloggers like this: