Najeriya

A yau Laraba kungiyar kwadago ta gudanar da yajin aiki da zanga-zanga a fadin Najeriya.

Kungiyar ta gudanar da yajin aikin ne sakamakon matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta.

An yi wa yajin aikin take da A Bar Talata Ya Shaki Numfashi.
Tun a baya kungiyar ta shirya tafiya yajin aikin bayan ƙarin kudin man fetur da aka samu a kasar.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya ayyana dakatar da cigaba da bayar da tallafin man fetur a Najeriya jim kaɗan bayna rantsar da shi a matsayin sanon shigaban ƙasar Najeriya.
Jihohi 36 sun fito tare da yin tattaki na zanga-zangar lumana, da nufin jan hankalin gwamnati donmin duba halin da ake ciki.
Kungiyar ta ce akwai bukatar a yi duba n atsanaki a kna lamarin, ganin yadda ma’aikata a Najeriya ke batar da kashi 70 na albashinsu a hanyar sufuri.
Kano
Kungiyar kwadago a jihar Kano ta gudanar da yajin aiki tare da zanga-zangar lumana a yau Laraba.
Jihar Kano ta bi sahun jihohin Najeriya wajen yin tattakin da kungiyar kwadago ta kasa ta shiya yi domin jan hankalin gwamnati a kan matsin rayuwa da ake ciki.
Shugaban ƙungiyar na jihar Kwamared Kabiru Inuwa ya yi karin haske wanda ya nuna gamsuwa a kan matakin da su ka ɗauka.
Ya ce ƙungiyar ta gamsu da matakin da aka ɗauka kuma haakan yayi tasiri donin yaa sanya gwamnatin ta waiwayi halin da aake ciki sabanin baya.
Ya kara da cewa kungiyar na da mataki daban-daban kuma wannan shi ne na farko sannan za su sake zama domin duba matakin da ya dace su dauka a gaba.
Abuja
Masu zanga-zanga a birnin tarayya Abuja sun ɓalle kofar shiga majalisar dokoki ta ƙasa tare da mamaye haaraba.
Hakan ya faru yayin da su ka fita don yin zanga-zangar lumana hadi da yajin aiki sakamakon tsadar man fetur da kungiyar ta ce ba ta gamsu da shi ba.
Mutane da dama sun yi cincirindo a harabar majalisar tare da kira ga gwamnati na ganin an duba halin da ake ciki wajen samar da saukin rayuwa a Najeriya.
Bayan gwamnati ta yi yunkurin raba naira biliyan 500 ga marasa galihu a kasar don rage radadin cire tallafin man fetur, kungiyar ta yi watsi da batun.
Idan ba a manta ba shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yan Najeriya jawabi a kan haalin da ake ciki har ma yaa yabawa kamfanoni masu zaman kansu da su ke tallafawa kasar wajen daukar mutane aikin yi.
Sannan ya ce za a yi amfani da kudaden wajen bayar da tallafi, samar da motocin sufuri da kuma amfani da kudin don farfado da bangaren ilimi ta yadda kowanne dan ƙasa zai smau ilimi ba tare da samun targaro a kan kudi ba.
Jawabin shugaban ya janyo cece ku ce a bakin al’umma wanda wasu ke ganin hakan ba zai wadatar ga yan kasar ba.