Rahotanni daaga jamhuriyar Nijar na nuni da cewar gwamnatin mulkin soji a ƙasar ta buɗe iyakokin ƙasar ga makoftansu biyar.

Sannan an bude iyakokin sama na kasar mako guda da rufewa bayan da sojoji su ka kwaci mulki daga hannun farar hula.
Mai magana da yawun mulkin sojin kasar ya sanar a gidan talabiji na kasar a yammacin Talata cewa, aan buɗe iyakokin ƙasar da su ka haɗa da Mali, Algeria, Burkina Faso, Libiya da kuma Chadi.

Iyakokin ƙasar da su ke cikin kungiyar ECOWAS kamar Najeriya da Benin za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Ƙungiyar ECOWAS ta zare kasashen Burkina Faso da Mali bayan nuna goyon bayansu ga mulkin soji a kasar Nijar.
An fara wani zaman tattaunawaa a Najeriya domin duba hanyoyin da za a bi don mayar daa mulki ga farar hula a ƙasar Nijar.
Sai dai helkwatar tsaro ta kasar Najeriya ta ce a halin yanzu, babu wani zaɓi a yanzu illa amfani da karfin mulkin soji don karɓe ikon mulki daga hannun sojojin Nijar tare da kayar da shi ga hambararren shugaban kasar Mohammed Bazoum.