Hukumar kula da tashoshin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da motocin haya a tashar jirgin sama da ke Abuja.
Hakan ya biyo bayan wani rikici da ya faru a tsakanin masu hayar motocin da aka fi sani da tasi.
Hukumomin kula da filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja sun ce dakatarwar ta fara aiki nan take kuma ta shafi dukkanin masu hayar motoci a ciki.
Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar Abdullahi Funtua ya buƙaci fasinjoji a tashar da su sami wata hanyar ta daaban.
Wani rahoto ya nuna cewa rikicin ya faru ne sanadin shugabanci ga masu hayar motocin wandaa kuma na iya shafar filin saukar jirgin.
Sai dai hukumomin kula da filin sun bai wa fasinjoji haƙuri a bisa matakin da su ka dauka.