Wata babbar kotu a jihar Kwara ta yankewa wani Kazeem Beiwa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun shi da laifin hallaka makocinsa.

Kotun ta kuma yankewa mutanen da su ka taimkaa masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru goma kowanne tare da biyan tarar naira dubu ɗari kowanne.
Alkalin kotun Justice S.M Akanbi ya ce kotu ta tabbatar da laifin kashe wani Olokose Olushola aa Illorin kwanaki kadan kafin bikinsa a shekarar 2021.

Sauran mutane hudu da ake zargin an yanke musu hukuncin bayan samunsu da laifin mallakar makami ba bisa ka’ida ba, garkuwa da mutum, kisan kai, da kuma mafani da sassan jikin ɗan’dam.

Mutum guda cikin masu laifin Kazeem Beiwa an yanke masa hukumcin kisa ta hanyaar rataya, ɗaurin rai da rai, daurin shekara goma a gidan yari da kuma biyan tara naira dubu dari.
Mutanen sun aikata laifin ne a watan Maris na shekarar 2021.
Kotun ta samu mutanen da laifin sannan ta yanke musu hukunci ga kowanne daga cikinsu.